Home 9 YAWAN SALLAR MACE MAI HAILA BAYAN TA SAMU TSARKI DA SHARI’A TA...

YAWAN SALLAR MACE MAI HAILA BAYAN TA SAMU TSARKI DA SHARI’A TA SANI   

1
0
               

 

 Wannan shi ne tsarin da mace za tayi sallah bayan ta samu tsarki.  

        
   1:- Idan mace ta samu tsarki kafin bullowar Alfijir. Za ta sallaci magariba da isha’i sannan ta yi Sallar asuba. 
 
 2:- Idan ta samu tsarki bayan bullowar Alfijir kafin fitowar rana. Zata sallaci asuba ne kawai.   
 
              3:- Idan ta samu tsarki bayan bullowar rana to ba zata sallaci asuba ba sai dai ta
 
 fuskanci azahar.     
4:- Idan ta samu tsarki bayan Sallar azahar kafin sallar la’asar zata sallaci azahar ne kawai.   
 
  5:- Idan ta samu tsarki bayan la’asar to zata sallaci azahar da la’asar.  
 
         6:- Idan ta samu tsarki bayan magariba kafin isha’i zata sallaci magarba kawai.    
 
     7:- Idan ta samu tsarki bayan isha’i zata sallaci magarba da isha’i.            
 
  A sanar da mata wannan a kuma yada sakon saboda muhimmancinsa. Allah ne mafi sani.
 
Allah yasa mudace yataimake mu duniya da lahira

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here