Home Rahoto Yawan fursunoni a gidajen gyaran hali na Najeriya ya kai 81,710 –...

Yawan fursunoni a gidajen gyaran hali na Najeriya ya kai 81,710 – NBS

7
0

Hukumar kididdiga ta ƙasa (NBS) ta ce yawan fursunonin da ke gidajen gyaran hali na Najeriya ya ƙaru zuwa 81,710 a zango na biyu na shekarar 2025, daga 69,946 da aka samu a 2017.

Rahoton NBS ya nuna cewa wannan na nuni da ƙaruwar kashi 16.82 cikin 100 a tsawon lokacin da aka duba.

Jihar Legas ce ta fi kowace jiha yawan fursunoni da adadin 9,209, duk da cewa ƙarfin ɗaukar gidajen gyaran halinta ya tsaya a 4,167, lamarin da ya nuna matsanancin cunkoso.

Sauran jihohin da ke da yawan fursunoni sun haɗa da Ogun, Kano da Enugu, yayin da Kogi, Bayelsa da Benue suka kasance jihohin da ke da mafi ƙarancin fursunoni.

Rahoton ya kuma bayyana cewa yawan fursunonin da ba a yanke musu hukunci ba ya ƙaru zuwa 53,790, sannan ƙarfin ɗaukar gidajen gyaran hali ya ƙaru zuwa 65,035. A cewar NBS, laifukan sata ne suka fi yawa wajen shigar fursunoni, yayin da laifukan cin hanci da rashawa suka fi ƙaranci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here