An ayyana jihar Akwai Ibom a matsayin jihar da ta tafi kowacce a jihohin Najeriya tsafta, kana daya daga cikin masu tsafta a Afrika, inji rahoton Daily Trust.
A cikin jerin da kafar yanar mai tasiri, ta duba tsaftan, ababen bude ido a Afrika, ta kuma gano Akwa Ibom ce tafi zama a tsaftace a fadin a Najeriya.
Jihar Akwa Ibom dai ita ce jihar da jama'a da dama suka fi kaunar gudanar da tarukan siyasa, addini, kasuwanci da sauran lamuran yau da kullum.
Jihar Sakkwato a Arewacin Nijeriya yaushe ne za ta karbi wannan kambin ganin yanda take daular Usmaniya akwai dimbin kayan tarihi da mutane suke ziyartar ta saboda su.
Akwai tsananin bukata gwamnati da hukumomi su yi wani kan tsaftar birnin Sakkwato ganin yanda al'ummarta ke son samun irin wannan kambi da addini da al'ada suka amince da shi, saboda tsafta na cikin cikon addini.