Yarjejeniyar tsagaita wuta: Isra'ila ta sako Falatsinawa 200

Yarjejeniyar tsagaita wuta: Isra'ila ta sako Falatsinawa 200

Kamar yadda yarjejeniyar dakatar da bude wuta ta tanada tsakanin Isra'ila da Hamas ta musayar fursunoni, bayan da Hamas ta saki rukuni na biyu na 'yan Ira'ila da ta yi garkuwa da su - wasu sojoji mata uku, ita ma Isra'ila a yanzu ta sako Falasdinawa 200 daga cikin wadanda take rike da su a kurkuku.

A wata sanarwa da hukumomin gidan yari na Isra'ila suka fitar sun ce: ''Bayan kammala dukkanin abubuwan da suka wajaba a gidajen yarin da kuma amincewar hukumomin siyasa an saki dukkanin 'yanta'addan daga gidajen yari na Ofer da Ktziot," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP da na Reuters, suka ce.

Ba kamar Falasdinawan da aka saki a makon da ya gabata ba, wadanda yawanci hukuncinsu na zaman gidan yari kadan ne, a wannan karon 121 daga cikin fursunonin suna kan hukuncin rai da rai ne - wasu bisa laifin kisan kai fiye da sau daya da ya hada da kisan farar hula 'yan Isra'ila.

Shekarun Falasdinawa fursunonin sun bambanta sosai - mafi kankanta da aka saki shi ne mai shekara 16, yayin da mai shekara 69 ya kasance mafi girma a cikinsu.

Daya daga cikin fursunonin ya shafe shekara 39 a gidan kurkukun Isra'ila, bayan da aka kama shi da farko a 1986.

Wadanda aka yanke wa hukuncin manyan laifuka mafiya tsanani ba sa cikin wadanda aka saki yau.

Kusan 70 daga cikinsu za a fitar da su daga Isra'ila ne inda za a bi da su ta Masar zuwa kasashe makwabta da suka hada da Qatar da Turkiyya, kafin a kai su Falasdinu.