'Yar shekara 3 ta rasu bayan da wani magidanci ya yi mata fyaɗe a Kano
Wani magidanci mai shekaru 49, mai suna Baba Idi, ya shiga hannun ƴan sanda a Kano bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 3 fyade, Khadija Adamu, wacce a ka fi sani da Yasmin.
An kama Bana Idi ne a ranar 29 ga watan Agustan 2022 biyo bayan mahaifin marigayiya Yasmin ya ƙorafi wajen ƴan sanda.
A wata hira da ya yi da SAHELIAN TIMES, kawun marigayiyar, Bilyamu Abubkar, ya bayyana cewa mahaifiyarta ta zo yi mata wanka, sai ta ga jini a al’aurar ta.
“Lokacin da mahaifiyarta ta tambaya, Yasmin ta tabbatar da cewa Baba Idi ne yake yi mata wani abu, kuma ya yi mata barazanar cewa zai kashe ta idan ta gaya wa mahaifinta,” in ji shi.
A baya dai baba idi ya taɓa shigar da marigayiyyar zuwa wani shagon gidansu yarinyar kuma ya yi mata fyade.
SAHELIAN TIMES ta ce ta samu kwafin rahoton likita, wanda ya tabbatar da an yiwa Yasmin fyade.
A cewar kawun, daga baya aka kai Yasmin shelkwatar ƴan sanda domin tantance wanda ake zargin.
Ya kara da cewa “Lokacin da ta gan shi, sai ta fashe da kuka, tana mai cewa ya yi alkawarin zai kashe ta kuma ya baiwa mage ta cinyeta,” in ji shi.
"Tun da ga nan Yasmin ta fara rashin lafiya, kuma banta jima ba bayan kwana uku ta rasu ta na ta nanata cewa “shi ne wanda ya ce zai kashe ni,"
managarciya