'Yansanda sun kama Dalibi bisa zargin kashe abokin karatunsa a Nasarawa

'Yansanda sun kama Dalibi bisa zargin kashe abokin karatunsa a Nasarawa
Rundunar ƴansanda a Jihar Nasarawa ta kama wani dalibi na Kwalejin Fasaha ta Tarayya, Nasarawa, bisa zargin kashe wani abokin karatunsa.
Mai magana da yawun rundunar, SP Ramhan Nansel, ya tabbatar da kamen a cikin wata sanarwa da ya fitar a Lafia, babban birnin jihar.
Ya ce kamen ya biyo bayan korafin wata mazauniyar unguwa, Madam Mercy Bassey, wadda ta bayyana wani rikici mai zafi da ya auku tsakanin ɗan haya a gidanta da abokinsa.
A cewarsa, bayan samun wannan rahoto, an tura masu bincike zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka iske Ibrahim Matthew, ɗalibi mai karatun ND2 a fannin Kimiyyar Kwamfuta a kwalejin, kwance cikin jini.
SP Nansel ya bayyana cewa an garzaya da wanda aka kashe zuwa Asibitin Kasa na Nasarawa, amma likitoci sun tabbatar da mutuwarsa saboda raunin da ya samu.
Ya ce wanda ake zargi, John Gambo, ɗalibi mai karatun ND2 a fannin Banking and Finance, ya shiga hannu, kuma ya amsa cewa ya kai hari ga mamacin da adda da wuƙa.
An kuma gano kayan aikin da aka yi amfani da su wajen kai harin, waɗanda suka kasance ɗauke da jinin wanda aka kashe.