'Yansanda sun kama ɓarawon da ya yaudari direban  da farfesu ya gudar masa da mota

'Yansanda sun kama ɓarawon da ya yaudari direban  da farfesu ya gudar masa da mota

Rundunar ƴansanda a jihar Legas, a yau Asabar ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da satar motar hayar zamani ta Uber bayan ya yaudari direban da farfesu ya tsere da motar.

Kakakin rundunar ƴansandan, SP Benjamin Hundeyin, ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a yau Asabar.

Hundeyin ya ce, rundunar ƴansandan a yankin Akinpelu ta samu rahoto a ranar 5 ga watan Yuli da misalin karfe 8:00 na dare daga wani direban Uber, wanda ba a ambaci sunansa ba.

Ya ce direban motar ya ba da rahoton cewa ya dauko fasinja ne, wanda kawai ya bayyana sunansa Ishaya, daga gidan man NNPC, Maryland, a cikin motarsa ​​Toyota Corolla zuwa wani otal da ke unguwar Oshodi.

Kakakin ya yi nuni da cewa, a otal din, wanda ake zargin ya saya wa direban abinci da farfesu da kuma lemo.

“A cikin haka ne, lokacin da wanda ake zargin ke neman audugar goge kunne, sai direban ya ba shi makullin motarsa ​​ya yi amfani da shi.

"Direban ya ci gaba da cewa wanda ake zargin ya sauka kasa bayan ya karbi motar ya tafi da motarsa daga inda ya ajiye ta.

“sai Ƴansanda da ke sintiri suka tare shi.

"Lokacin da ya kasa bayar da gamsasshen bayani game da mallakar motar, sai aka kama shi," in ji shi.

Hundeyin ya ci gaba da cewa yayin da jami’an ‘yan sandan ke shirin kai wanda ake zargin zuwa ofishin, direban ya zo wurin ya ga motar.

Ya ce an tsare wanda ake zargin domin ci gaba da bincike.