Ƴansanda sun fara zanga-zangar neman ƙarin albashi na masu aiki da waɗanda su ka yi ritaya
'Ƴansanda sun fara zanga-zangar neman ƙarin albashi na masu aiki da waɗanda su ka yi ritaya
An hangi Omoloye Sowore, ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, ya jagoranci gungun masu zanga-zangar domin neman a inganta rayuwar jami’an ƴansanda a Najeriya.
Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnati ta duba halin kuncin da ƴansanda ke fuskanta, musamman yadda albashinsu da fansho ke ƙasa da kima.
Hakazalika an hango Bello Galadanci, wanda ake wa laƙabi da Ɗan Bello, mazaunin China kuma ɗan gwagwarmaya mai rabin fallasa cin-hanci da masu mulki ke yi, a wajen zanga-zangar.
A ga dai masu zanga-zangar ɗauke da kwalaye da rubutu iri-iri na neman a bunƙasa walwalar su.
managarciya