YANDA ZA KI HADA PINACOLADO NA MUSAMMAN
PINACOLADO
INGREDIENTS
Kwakwa
Abarba ko leman zaki
Sugar
Flavour na abarba
METHOD
Da farko zaki goga kwakwa da abun goga kuɓewa,se ki markaɗa a blender sai ki zuba ruwan sanyi ki tace da rariya,se ki markaɗa abarba ko (leman zaƙi) ki tace ta ki zuba a kwano,ki dafa sugar da ruwa ki barshi ya huce.
se ki haɗa kwakwa da abarba guri ɗaya ko leman zaƙi ki zuba suger da flavour ki juya sosai asa a Refrigerator yayi sanyi.
Wannan lemun ana haɗa shi ne lokacin da za’a sha, idan kuma aka haɗa aka sa shi a (Refrigerator) za'a ga man kwakwar ya taso, ba lalace wa yayi ba sai a ƙara markaɗawa.
MRSBASAKKWACE.
managarciya