YANDA ZA KI HADA COBB SALAD MAI DADIN GASKE
@BASAKKWACE'Z KITCH
COBB SALAD
INGREDIENTS
Masara
Naman rago
Naman kaza
Gwanda
Fiya
Latas
Tumatur
Albasa me lawashi
METHOD
Da farko aunty na zaki dauko fiyan ki, ki wanke ki fere ki yanka ta a tsaye, se ki d'auko gwandar ki ki wanke ki fere bayanta ki yanka, se ki dauko tumatur d'in ki ki wanke ki yanka, se ki dauko dafaffiyar masaran ki ki cire ta a totuwan ta, se ki dauko gasashiyar naman ragon ki ki yan-yanka shi k'anana, se ki d'auko gasashiyar tsokar kazar ki ki yanyankata kananu
Se ki dauko plate ko bowl ki shinfida falle fallen latas ki shimfid'a akan bowl din ko farantin se ki jera ingredients d'in ki, kina iya ci da shinkafa ko hakanan kawai, yana rage tumbi kuma yana gyara jiki, yasa jiki ye fresh.
MRSBASAKKWACE
managarciya