BASAKKWACE’Z KITCHEN
SOYAYYAR SHINKAFA
INGREDIENTS
Shinkafa
Karas
Koren wake
Tattasai
Attarugu
Albasa
Magi
Kori
Garin tafarnuwa da citta
barkono
butter
METHOD
A ɗora tukunya da ruwa a cikinta har sai ya tafasa sannan a Ɗauko shinkafa a wanke a zuba a ciki. Idan ta dan tafasa kamar mintina talatin , sai a sauke a wanke da ruwa a tsame ta a matsami ruwan ya tsane.
A sake ɗora wata tukunyar a wuta sannan a zuba butter a yayyanka albasa a zuba ta soyu sosai. Sannan a ɗauko garin citta da tafarnuwa da magi da kori sai a ci gaba da gaurayawa. Sannan a zuba su karas da koren tattasai da attarugu da shinkafar sannan sai a gauraya sai a rage wuta a rufe tukunyar da marufi na tsawon minti 20 sannan a ɗauko busashen barkono wanda ba a daka ba a sa a sama,ya ƙara minti goma sannan a sauke
MRS BASAKKWACE
