KAYAN HAƊI
Farin garin rogo
Attarugu
Yankakkiyar albasa
Warm water
Farin magi
Ƙuli
Yaji
Seasoning cubes
YADDA ZAKI HAƊA
Da farko zaki tankade garin rogonki sai ki zuba shi a mazubi mai kyau, ki zuba jajjagaggen tarugu, yankakkiyar albasa da farin magi sai ki dinga zuba ruwan zafi a hankali kina kwaɓawa da hannunki, ki yi kwabin dai-dai kada ya yi tauri sosai kada kuma ya cika ruwa, dai-dai yadda zaki iya mulmulawa dai.
Daga nan sai ki mulmula ki dinga faɗa da yatsunki kina ajiyewa a kan tray.
Zaki ga zanen yatsunki yana fitowa a bayan ƙosan.
Ki ɗora kwanon suya a wuta ki zuba mai ya yi zafi sai ki dinga ɗauko ƙosanki kina sakawa a ciki, ki dinga juya gefe da gefe idan ya yi kalar golden sai ki cire ki tsane a gwagwa.
Ƙosai ya kammala, daga nan kawai sai ki daga ƙuli yaji da maginki, idan ya daku ki kwashe ki dinga dangwala ƙosan a ciki.
Enjoy it.
RUKY’S BAKERY





