Yanda Za Ki Haɗa Dambun Nono
Abubuwan da ake bukata:
Gero
Madaran ruwa
Sugar
Kankara
Ayaba.
Yanda zaki hada:
Zaki samu surfaffen geron ki ki wanke ki gyara shi da kyau, Sai ki Dora kan wuta ki dafa shi Sai ya dahu, kina yi kina jujjuya shi kina Kara ruwa, Yana dahuwa Yana Kara kumburi.
Idan ya dahu Sai ki sauke, ki barshi ya huce Sai ki dauko madara ki zuba, ki yayyanka ayaban ki Sai ki zuba ki saka sugar daidai dandanon ki.
Sai ki dauko kankara ki fashe ki zuba a Kai.
Tested nd trusted
Daga Safiya Usman
managarciya