Wasu gungun ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun kashe maigarin Kulodo a Ƙaramar Hukumar Bodinga ta Jihar Sokoto, Alhaji Abubakar Tudu, da babban ɗansa tare da wasu mutum biyar a hare-haren da suka kai ƙauyukan Kulodo da Kwance.
Harin ya faru ne ranar Juma’a yayin da mazauna yankin ke gudanar da sallar La’asar.
Wata majiyar tsaro ta ce ’yan bindigar sun shiga ƙauyukan a kan babura, inda su ka riƙa harbe-harbe, sannan su ka kwashe dabbobi masu yawa zuwa cikin dajin Jihar Zamfara.






