‘Yán tà’àdda a jihar Katsina, sun kai harí inda suka kashe wasu mahalarta ɗaurin aure, tare da sace amarya da wasu mutane 17.
Kamar yadda Katsina Post ta samu daga Alfijir Radio, Harin ya faru ne a yankin Unguwar Nagunda da ke ƙaramar Hukumar Ƙanƙara, washegarin da gwamnatin jihar ta bayyana dalilan shirinta na sakin mutum 70 da ake zargi da laifukan ta’addanci a faɗin jihar.
Sai de, daga bisani mutum 8 daga cikin waɗanda aka sace sun samu kuɓuta, inda suka koma wurin iyalansu a ranar Litinin.
Kazalika, ‘yànbindígar sun kashe wani mutum a ƙauyen Kafa da ke kan babbar hanyar Kankara zuwa Sheme da ke ƙaramar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina.






