'Yan Wasan Hausa  13 Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Tinubu 

'Yan Wasan Hausa  13 Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Tinubu 

Jam’iyya mai mulki a Nijeriya ta APC, ta saki jerin sunayen mambobin yakin neman zaben shugaban kasa na sashen Mata a ranar Asabar. 

APC ta sanar da nada Matar shugaban kasa Aisha Buhari a matsayin wadda zata jagoranci mata a kamfen.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Rinsola Abiola, diyar marigayi Cif MKO Abiola, kuma jigo a jam’iyyar APC ta fitar.
Wasu jaruman wasan kwaikwayon Kannywood kimanin 13 sun samu shiga jerin mambobin kwamitin. 
Fati Nijar, Mansurah Isah, Saratu Daso, Samirah Ahmad, Teema Makamashi, Fati Karishma, 
Hajiya Nas, Ummi Gombe, Kyauta Dillaliya, Hadiza Kabara, da  Rahama Sadau.