'Yan wasan ƙwallon Zamfara sun shiga yajin aiki

'Yan wasan ƙwallon Zamfara sun shiga yajin aiki
 
'Yan wasan ƙwallon Zamfara sun shiga yajin aiki
 
 
Ƙungiyar wasan ƙwallon ƙafa na jihar Zamfara ta  tsundama cikin yajin aiki kan ƙin biyansu albashi da gwamnati ta yi don haka suka ga ya dace su ɗauki irin wannan matakin don nuna ɓacin ransu.
Ɗaya daga cikin 'yan wasan ƙwallon ƙafar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce gwamnati ta ɗauke su ne su riƙa shura ƙwallo amadadin jihar a gasar wasan ƙasa ajin ƙwararru mai daraja ta biyu (Nigerian National League).  
Ya ce ba su da wata sana'a da suka dogara da ita don kula da kansu da iyalansu sai ƙwallon ƙafa don haka bai kamata gwamnati ta yi wasa da sana'arsu wurin biyan alhakinsu.
Ya yi kira ga gwamnatin jiha ta dube su da idon basira don magance masu halin da suke ciki a biya musu haƙƙinsu dake hannun gwamnati.
 
Managarciya ta tuntuɓi hukumar wasanni ta jihar Zamfara kan lamarin yajin aiki amma jin tabakin hukumar ya ci tura.