'Yan wasan ƙwallon ƙafa za su samu ƙarin albashi a Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim, Gusau.
A kokarin da Gwamnatin jihar Zamfara keyi Karkashin jagorancin gwamna Matawalle na ganin ta inganta harkar wasannin a Jihar ,yanzu haka tana shirin karawa 'Yan wasan karin albashi daga N 400,00 zuwa N50,000.dan kara katfafasu akan gagarumar nasara da suke samu a fagen wasannin.
Mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin wasanni Hon Habib Yuguda,Gusau ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau.
Hon Yuguda ya Kuma bayyana cewa, yanzu haka Gwamnati zata kashe naira biliyan N1.5 wajan gina filin wasa na Zamani a Gusau babban birnin jihar.
'Ya ce filin wasan idan aka kammala shi zai kasance irinsa na farko a daukacin yankin Arewa maso yammacin Najeriya domin zai kasance mai inganci a duniya.
Ya ce gwamnatin jihar ta kuma amince da kashe Naira miliyan 100 don gyarawa da kuma sake gina filin wasa na tunawa da Sardauna da ke Gusau domin bunkasa harkokin wasanni a jihar.
Ya kara da cewa an kuma dauki sabbin ‘yan wasa a kungiyar kwallon kafa ta Zamfara United domin bunkasa damarta na lashe kofi a gasar ta bana.
Hon Yuguda ya ce anaba ‘yan wasa albashi mai kyau da alawus alawus don bunkasa kwazon su.
Habib ya ce wasanni shi ne babban fifikon gwamnatin jihar saboda muhimmancinsa ga matasa.
"Wasanni da akeyi yana Kara kawo zaman lafiya a tsakanin jama'a a cikin al'umma da sada zumuncii," in ji Habib.
Ya kuma yi kira ga matasa a jihar da su dukufa wajan shiga harkar wasannin na kowane sashe da ya taimaka wajan cinmoriyar sa kuma rayuwa ta ingnta.