'Yan Ta'addan Lakurawa Sun Sake Sabon Ta'addanci a Kebbi 

'Yan Ta'addan Lakurawa Sun Sake Sabon Ta'addanci a Kebbi 

 
Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ta’addan Lakurawa ne sun kashe ƴan sanda biyu a jihar Kebbi. Ƴan ta'addan na Lakurawa a yayin harin sun kuma sace shanu sama da 200 a ƙauyen Natsini da ke ƙaramar hukumar Argungu a jihar Kebbi. 
 
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 11:00 na dare.
 
Rahotanni daga ƙauyen sun bayyana cewa, ƴan sandan suna a wajen wani shingen binciken ababan hawa da ke kan titin Augie/Kangiwa, lokacin da lamarin ya auku. Ƴan ta’addan da yawansu ya kai 50 a kan babura sun kai musu hari inda suka kashe biyu daga cikinsu kafin su shiga ƙauyen su sace shanu. Ƙauyen Natsini yana kan titin Augie/Kangiwa sannan yana da tazarar kilomita biyar daga garin Argungu. Wani ɗan yankin mai suna Abubakar Augie ya bayyana cewa shanun da aka sace na wani fitaccen ma’aikacin gwamnati ne mai suna Lawali Black. 
"Ƴan Lakurawan sun fi 50 akan babura, bayan sun ci ƙarfin ƴan sandan da ke shingen binciken, sai suka je inda aka ajiye shanun a cikin gonarsa, suka tafi da su." - Abubakar Augie 
Shugaban karamar hukumar Argungu, Aliyu Gulma ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce tuni majalisar ƙaramar hukumar ta gudanar da taron tsaro kan lamarin, kuma gwamnatin jihar ta umarci jami’an tsaro da su bi sahun ƴan ta’addan da nufin ƙwato shanun da aka sace.