'Yan ta'adda sun sako ragowar mutane 23 na harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

'Yan ta'adda sun sako ragowar mutane 23 na harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

A yau Laraba ne ƴan ta’adda su ka sako sauran mutane 23 da su ka yi garkuwa da su a harin jirgin ƙasan da ya taho da ga Abuja zuwa Kaduna.

Gidan Talabijin na Channels TV ya rawaito cewa sakataren kwamitin da ke kula da harkokin tsaro na kasa, Usman Yusuf ne ya bayyana hakan.

Yusuf ya ce an sako mutanen ne da misalin karfe 4 na yammacin Laraba.

Ya ce kwamitin ya karɓi wadanda ƴan ta’addan Boko Haram suka yi garkuwa da su a wani hari da suka kai wa wani jirgin kasan fasinja a Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022.

‘Yan ta’addan da suka kai hari kan titin AK9 da ke Kaduna, sun riƙa sakin rukuni-rukuni na waɗanda su ka rike har zuwa  ranar 19 ga Agusta, 2022.

Maharan sun tarwatsa titin jirgin tare da jefa bam a cikin jirgin da ke tafiya, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da fasinjoji sama da 60. Harin da ba a taba yin irinsa ba ya janyo cece-ku-ce tsakanin kasashen duniya da na kasa baki daya.

‘Yan uwa da ke cikin rudani sun yi zanga-zanga sau da yawa don neman a sako ‘yan uwansu.