'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki a Zamfara  Sun Halaka Mutum 7 da Sace 20

'Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki a Zamfara  Sun Halaka Mutum 7 da Sace 20

 

An kashe mutum bakwai yayin da wasu ƴan ta’adda suka yi garkuwa da wasu mutum kimanin 20 a wani hari da suka kai a jihar Zamfara. Ƴan ta'addan sun kai harin ne da yammacin ranar Alhamis a ƙauyen Nasarawa Godel da ke ƙaramar hukumar Birnin Magaji ta jihar. 

Mutanen yankin da suka zanta da jaridar Premium times sun ce ƴan ta’addan sun zo ne a cikin motocin Toyota Hilux, saɓanin babura da suke hawa. 
"Muna da gawarwaki bakwai a ƙidaya na ƙarshe. Wasu da dama sun samu munanan raunuka. Yawancin waɗanda aka sace mata ne. An jefa al’umma gaba ɗaya cikin ruɗani. "Ƴan ta’addan waɗanda ake kyautata zaton ƴan tawagar Gwaska Dankarami ne, sun afka ƙauyen ne da misalin ƙarfe 6:00 na yamma cikin motocin ƙirar Hilux guda uku suka nufi hanyar fita daga cikin ƙauyen. 
"Yana daga cikin tsare-tsarensu na yaudara. Lokacin da muka ga suna tuƙa mota zuwa hanyar Kasheshi Kura, ƙauyen da ke makwabtaka da mu, yawancin mu muna tunanin 'yan ta'adda za su kai hari a wani ƙauyen."
Ya ce sun zagaya ta hanyar waje inda suka fara harbi ba kakkautawa a lokacin da akasarin ƴan banga da ke ƙauyen suka fita domin taimakawa ƙauyen Kasheshi Kura. 
Wani mazaunin garin wanda ya bayyana sunansa da Mubarak, ya ce an kashe abokinsa tun na yarinta a harin. 
"Abin kunya ne yadda ƴan ta'adda za su shigo gari su fara harbin mutane. Sun yi tsawon sa’o’i uku ba tare da wanda ya kare mu ba. Legit Hausa ta kasa jin ta bakin kakakin ƴan sandan jihar Zamfara Yazid Abubakar kan harin, saboda bai dawo sa amsar saƙon da aka tura masa ta wayarsa ba.