'Yan Ta'adda Ba Za Su Sake Tasiri A Nijeriya Ba----Shugaba Buhari
Shugaba Buhari ya ce, ‘‘Saboda akwai yunkurin da suka yi wajen ruguza Nijeriya baki daya, amma Allah bai yarda ba. Kuma cikin ikon Allah ga Nijeriya nan ta sake komawa yadda take a baya." Har wala yau, Buhari ya yaba da kokarin sojojin Nijeriya tare da hadin gwiwa da Yan-sanda bisa sadaukarwar da suka nuna wajen kare mutuncin Nijeriya.
Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya ce yan ta'adda ba za su sake yin wani katavus da sunan tasiri ba, saboda yadda gwamnatinsa ta yi musu raga-raga, inda kuma ya kuma bukaci yan Nijeriya su ci gaba da bai wa jami'an tsaro cikakken goyon baya da hadin kai tare da bin doka da oda.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci Fadar Sarkin Damaturu a jihar Yobe, Mai Martaba Hashimi El-Kanemi II, a ziyarar aikin bude wasu manyan ayyukan da gwamnatinsa tare da ta jihar Yobe suka aiwatar, inda ya ce, gwamnati za ta ci gaba da kare yancin kowane yaro dan Nijeriya wajen samun ilimi, musamman yan gudun hijira wadanda rikicin Boko Haram ya raba da garuruwan su.
‘‘Wanda zan iya cewa wata hudu masu zuwa, zan bar ofis, kuma zan ci gaba da abubuwan da suka kamata, sannan kuma ina da burin zan koma gefe in yi ritaya cikin aminci."
‘‘Sannan kuma dole mu gina kyakkyawar fata a zukatanmu game da kasarmu, saboda abu ne mai muhimmanci mu tabbatar cewa bangaren tsaro da tattalin arziki sune kan gaba."
‘‘Haka kuma abubuwa da dama sun faru a matsayinta na kasa, wanda nake kara kira gareku ku ci gaba da juriya tare da tsayin-daka ba zamu bari wani ya sake hargutsa mu ba." Ya nanata.
Dangane da yadda aka samu ci gaba a sha'anin tsaron Arewa Maso Gabas, shugaban Nijeriya ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni da takwaransa na jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, bisa aiki tukuru wajen sake farfado da makarantu, asibitoci hadi da muhimman wuraren da yan ta'adda suka lalata a jihohin.
Shugaba Buhari ya ce, ‘‘Saboda akwai yunkurin da suka yi wajen ruguza Nijeriya baki daya, amma Allah bai yarda ba. Kuma cikin ikon Allah ga Nijeriya nan ta sake komawa yadda take a baya."
Har wala yau, Buhari ya yaba da kokarin sojojin Nijeriya tare da hadin gwiwa da Yan-sanda bisa sadaukarwar da suka nuna wajen kare mutuncin Nijeriya.
Bugu da kari, shugaban kasa ya nanata cewa a matsayin sa na wanda ya yi gwagwarmayar hadin kan Nijeriya a lokacin yakin Basasa, ya ce babu yadda za a yi ga wanda ya tsinci kansa a wancan yanayin "Ace zai amince wani mutum ya sake raba kan yan kasa."
A nashi bangaren, Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya shaida wa shugaban kasa cewa, sakamakon kamarin rikicin Boko Haram, ita ma Fadar Sarkin Damaturu bata tsira daga mamayar yan ta'addan ba.
‘‘Haka zalika kuma, yau gashi zaman lafiya ya samu a kowane bangaren jihar Yobe, babu wani yanki a jihar da yake a hannun Boko Haram."
‘‘Wanda kafin hakan, a baya da za ka ajiye dala biliyan daya a wannan Fadar ka ce wani ya zo ya dauka, babu mutumin da zai yi kasadar zuwa kusa da ita. Amma bayan kasancewarka Shugaban Kasa, abin ya zama tarihi, wanda al'ummar jihar Yobe ke more yancin zaman lafiya da suka samu."
A nashi jawabin, Sarkin Damaturu ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Kasa bisa inganta harkar tsaro a Nijeriya, inda ya ce, ‘‘Saboda ko shakka babu mu a nan jihar Yobe ganau ne, dangane da qoqarin ds gwamnatinka tayi na kawo ci gaba a qasa."
Bayan ziyarar Fadar Sarkin Damaturu, tawagar Shugaba Buhari ta zarce wajen bude ayyukan da gwamnatin jihar Yobe wajen aiwatar kana da karin wasu ayyuka wadanda Ma'aikatar Yan -sanda ta aiwatar a jihar.
Ayyukan da suka hada da bude Shalkwatar Rundunar Yan-sanda, Asibitin Yan-sanda tare da hanyoyi da Makarantar Sakandire ta Yan-sanda, wadanda aka kammala aikin su, a karkashin Safeto-Janar, Usman Alkali Baba.
Har wala yau kuma, Shugaban Kasa ya bude filin jirgin sama (Muhammadu Buhari International Cargo Airport) Kasuwar Zamani a Damaturu, Asibitin kula da lafiyar mata da yara a Asibitin Koyarwa ta Jami'ar jihar Yobe, kana da bude Rukunin Gidaje 2600 wadanda jihar ta gina a fadin jihar tare da Makarantar Mega School a Rukunin Gidaje na New Bra-Bra, wanda Gwamna Buni ya gina.
managarciya