'Yan siyasa ne ke taimaka wa masu zanga-zanga domin kawo ruɗani a Najeriya - Shettima
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya bayyana cewa shugaban kasar na da aniyar ganin ya tallafa wa al’ummar arewacin kasar, sai dai akwai mutanen da ke kawo cikas.
Shettima ya fadi hakan ne a cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa a ranar Alhamis.
Mataimakin shugaban ya ce shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu na sane da halin da al'umma ke ciki, kuma yana tausaya masu, "Insha Allah gwamnati na kawo tsare-tsaren ganin cewa la'ummarmu an ɗauki matakin ƙarfafasu."
Mataimakin shugaban Najeriyar, ya ce sun ɗauki matakai da suka haɗa da cire ton 42,000 na hatsi domin tallafa wa al'ummar ƙasar da kuma ƙarin mafi ƙarancin albashi daga 30,000 zuwa 70,000.
Mataimakin shugaban Najeriyar, Shettima ya ce suna da kyakkyawan niyyar samar da aikin yi ga matasan ƙasar, "An kawo tallafin karatu, kuma ba sai kasan wani ba, kowane ɗan Najeriya, yana da haƙƙin samun tallafin biyan kuɗin makaranta, Insha Allah zamu samar wa ƴaƴanmu aiki a Arewa."
Shettima ya ce sun san halin da matasan suke ciki, kuma nan ba da jimawa ba za su yi taron gwamnoni da attajirai da masu ruwa da tsaki na arewacin ƙasar domin fitar da wani tsari da zai taimaka wa yankin.
"Taron da za mu yi ba na shan shayi bane, da cin kaji, muna son a gani a ƙasa ne, kowane attajiri da yake son ya yi taimako ya faɗi me zai kawo, kuma na yi imanin za su taimaka, za kuma mu gayyaci Rabi'u Musa Kwankwaso."
Shettima ya ce lokaci ya yi da manyan arewacin Najeriya za su haɗa kai, "Duk ɗan siyasar da yake kishin arewa, ba wai sai ya zama mamba na APC ba, babu banbancin addini babu banbancin siyasa ko ƙabila, iya ruwa fidda kai, mu zo mu haɗa kai, idan mun san me muke yi ba mu da matsalar talauci a arewa saboda Allah ya albarkace mu da komai."
Arewacin Najeriya dai na fama da mastalar tsaro , lamarin da ya raba wasu al'ummomin yankin da muhallansu, ya kuma hana manoma da dama yin noma a gonakinsu.
Duk da iƙirarin hukumomi na cewa suna ƙoƙarin ganin shawo kan matsalar, sai dai wasu ƴan ƙasar na ganin cewa kamar ba da gaske gwamnati ke yi ba musamman idan aka yi la'akari da rahotannin kashe al'umma da sacewa domin kuɗin fansa da kullum ake samu daga arewacin Najeriyar.
managarciya