'Yan sandan sun kama  fulani 47 a yunkurin kisan kai cikin Polytechnic Birnin Kebbi

'Yan sandan sun kama  fulani 47 a yunkurin kisan kai cikin Polytechnic Birnin Kebbi

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta kama wasu makiyaya guda 47 bisa laifin aikata laifuka da kuma yunkurin kisan kai sakamakon farmakin da suka kai wa makarantar firamare ta Waziri Umaru Federal Polytechnic, Birnin Kebbi.

A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Nafiu Abubakar ya fitar a ranar Litinin din da ta gabata, lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na safiyar ranar 4 ga watan Fabrairun 2025, inda wani mazaunin unguwar Ruggar Labana mai suna Abubakar Nabande ya hada baki da wasu wajen shiga harabar makarantar da karfi.

Makiyayan dauke da kayan yanka da sanduna, sun kutsa katangar makarantar, inda suka kai sama da shanu 300 cikin harabar makarantar. Sun zarce zuwa rukunin ma'aikatan, suna lalata ciyawa da aka adana," in ji sanarwar.

Ya kuma kara da cewa a lokacin da ma’aikatan polytechnic da jami’an tsaro suka yi yunkurin korar masu kutse, an yi zargin makiyayan sun rikide zuwa tashin hankali.

Da samun rahoton kwamishinan ‘yan sandan Bello M. Sani da kan sa ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa wurin domin tantance su a nan take. Bayan bincike, jami'an sun kama mutane 47 da ake zargi da hannu a harin.

Tuni dai aka gurfanar da wadanda ake zargin a gaban l gaban kuliya.