Home Manyan Labaru ‘Yan sanda sun tabbatar da Lakurawa sun kashe mutane 33 a jihar...

‘Yan sanda sun tabbatar da Lakurawa sun kashe mutane 33 a jihar Kebbi

2
0

 

Rahotanni daga Kebbi na cewa ‘yan ta’addar Lakurawa sun kashe mutane sama da 30 a wasu hare-hare da suka kai wa wasu kauyukan jihar bakwai.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kebbi SP Bashir Usman ya ce lamarin ya faru a yankin Bui karamar hukumar Arewa a maracen ranar Laraba, kuma tuni aka tura jami’an tsaro domin bin bayan ‘yan ta’addar.

Bashir ya ce ‘haɗin guguwar jami’an soja da sauran jami’an tsaro an ba za su wuraren don dawo da kwanciyar hankali.

“Muna baƙin cikin rasa rayukan Mutane 33 da ba su ji ba su gani ba, in da muke miƙa ta’aziyar mu ga iyalan margayan da mutanen ƙaramar hukumar Arewa gaba ɗaya.”

Ya ce a binciken da aka yi an tabbatar da ‘yan bindigar Lakurawa ne suka shiga yankin domin satar shanu, ɓatagarin sun yanko daga yankin ƙaramar hukumar Gudu a Sakkwato.

Mutanen ƙauyen  Mamunu, Awasaka, Tungan Tsoho, Makangara, Kanzo, Gorun Naidal, da  Dan Mai Ago sun haɗu don kare kansu a lokacin da maharan suka kawo farmakin kafin wannan ƙazamar nasara da suka samu.

Ya ce akwai buƙatar cigaba da aiki tare a tsakanin jami’an tsaro kan waɗannan hatsabiban ‘yan bindiga. Ya nemi mutanen farar hula da su riƙa ba da bayanin duk wani motsi da ba  su yarda da shi ba,  ga jami’an tsaro su daina tunkarar ‘yan bindigar kai tsaye hakan nada hatsari.

Ya ce hukumar tana tsaye sai ta tabbatar da kawar da ɓaatagarin da masu taimakon su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here