'Yan sanda sun kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga tare da AK-49 da harsasai

'Yan sanda sun kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga tare da AK-49 da harsasai
'Yan sandan jihar Sakkwato sun sanar da kama ƙasurgumin ɗan bindiga hɗi da muggan makamai da harsasai a wani samame da aka kai bayan samun bayanan sirri.
A satin da ya gabata ne  jami'an 'yan sanda da aka ware domin yaƙar garkuwa da mutane suka samu sahihan bayanan sirri wanda ya kai ga kama Buba Magaji dake ƙauyen Julirkol a ƙaramar hukumar Silame a jihar Sakkwato.
"Kama Magaji ya faru ne kan kusancinsa da 'yan bindigar Lukurawa da ke addabar yankin sun hana zaman lafiya a ƙaramar hukumar Wamakko da Binji Silame da Yabo.
"A lokacin binciken wanda ake tuhuma ya karɓa laifin cewa yana cikin masu aikata manyan laifi a yankin har ya sanar da  in da bindigar AK-49 take a ɓoye cikin daji anan take aka dauko."
A bayanin da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yanda na Sakkwato DSP  Ahmad  Rufa'i ya fitar ga manema labarai ya ce a binciken da aka yi an samu bindigar AK -49 guda da aljihun harsasai(magazine) guda da harsasai masu rai guda 22.
Ya kara da cewa kama Buba da miyagun makamai nasara ce da jami'anmu ke samu,  an fadada bincike don gano maɓoyar sauran masu aikata laifin tare da wannan ɗan bindigar da suka addabi yankin.
Ya ce Kwamishinan 'yan sandan jiha ya baiwa mutane tabbacin kawar da aikata manyan laifuka a yankin su dai cigaba da baiwa jami'an 'yan sanda goyon baya da haɗin kai.