Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi sun nasarar kama uwa mai shekara 20 da ta haifi jaririya ta kuma turbude ta da rai don gundun abin kunya.
A ranar Alhamis jami'in hulda da jama'a na rundunar CSP Nafi'u Abubakar ya fitar da bayani ga manema labarai kan nasarar da suka samu a wurin dakile aiyukkan barna a jihar.
Ya ce rundunar 'yan sandan ta kama wata mata mai suna Maryam Atiku dake da shekara 20 tana zaune a unguwar Nasarawa garin Kamba cikin karamar hukumar Dandi a Kebbi, bayan ta haifi jaririyar mace sai ta daure jinjirar da ƙyallen atamfa da ta yanke gida uku, ta rufe bakin yarinya da kafadarta, a haka ta dauke ta zuwa dajin Malam Yero ta gina rame mai tsayi ta sanya yarinyar da rai ta rufe ta wuce abinta, a ganinta asirinta ya rufe.
Ya cigaba da cewa "Kwana daya da wannan mummunan aikin da ta yi Alhaji Kabiru Muhammad ya tafi gonarsa dake ƙauyen Malam Yero, yana cikin gonar ne sai ya lura da angine kasa wuri-wuri an yi kamar sabon Kabari, bai yi wata-wata ya kira makwabtansa suka taimaka masa aka fito da yarinyar a raye. Anan take suka garzaya da jinjirar zuwa babbar Asibitin Kamba in da aka kula da ita har ta dawo lafiya lau," a cewarsa.
Ya ce bayan sanar da 'yan sanda ne sashen kula da binciken manyan laifuka a Birnin Kebbi suka shiga bincike har suka yi nasarar kama wadda ake tuhuma a binciken da aka yi kuma ta karba laifinta.
Kwamishinan 'yan sanda CP Bello M Sani ya ce ba za su taɓa lamunce walakanta kananan yara ko bautar da su, kowane jinsin mace dana miji a jiha.
CP ya yi kira ga uwaye da shugabannin al'umma su ji tsoron Allah su tsare yaransu don gudun tarwatsa rayuwarsu a rasa gobe mai kyau don talauci ko wasu dalilai na daban.
Ya ce za su kai wadda ake tuhumar a Kotu da zaran an kammala binciken da hukumar ke yi.
Uwar gidan Gwamnan Kebbi Hajiya Zainab Nasare Nasir ta bayar da gudunmawa ga kulawa da yarinyar da kuma wanda ya aminta da ya rike yarinyar a hannunsa waton Alhaji Kabiru Muhammad.
Mutane da dama sun yi al'ahabin ganin jinjirar yarinya ta yi kwana ɗaya a cikin kasa ba ta mutu ba, sun kira wannan baiwa ce ta Allah da ya yi kan yarinyar.