'Yan sanda sun kama mutum biyu kan zargin yiwa yarinya fyaɗe a jihar Kebbi

'Yan sanda sun kama mutum biyu kan zargin yiwa yarinya fyaɗe a jihar Kebbi
'
'Yan sanda a jahar Kebbi sun kama mutum biyu da aka zargi da yi wa ƙaramar yarinya fyaɗe a Kebbi, a kokarinsu na hana cin zarafin ƙananan yara ne suka samu nasarar cafke mutanen.
A satin da ya wuce ne wata yarinya Vina Shehu mai shakara 10 a Unguwar Bedi ƙaramar hukumar Zuru, mahaifiyarta ta aike ta karbar sako akan hanyar ne Amos Jondo Maliki dake unguwa daya ita ya sa ta a dakinsa ya sadu da ita.
Haka kuma a wannan satin wata Nana Aisha Aminu Wala mai shekara biyar a unguwar Goribbu ta je shagon Mansur Sani mai Shekara 48 shi ma unguwar su daya domin ta sayi minti(alewa), a cikin cinikin ne ya durkusar da ita a shagon ya rika sanya yatsansa cikin al'urarta.
In an kammala bincike hukumar 'yan sanda za su gabatar da mutum biyu da ake tuhuma a gaban kotu.
Kwamishinan 'yan sanda na Kebbi CP Bello M Sani ya jinjinawa Kwamishinan Shari'a Barista Junaidu Bello kan daukar lamarin cin zarafin jinsin ba abu ne na wasa ba a jihar.
CP Bello ya yi tir da faruwar lamarin ya kuma ba da tabbaci ga mutane za su cigaba da kare jama'a musamman mabukata a cikinsu tare da alkawalin yi wa kowa adalci.
 Ya jaddada hukumar ba za ta lamunce cin zarafin yara kanana ta kowace siga. Akwai bukatar uwaye su cigaba da kula shige da fice na yaransu, a kuma kawo rahoton duk wani cin zarafi da aka yi a ofis na 'yan sanda mafi kusa.
Matsalar fyade a cikin al'umma tana kara ta'azara in da akwai bukatar gwamnatoci a Nigeria su dauki mataki tsattsaura ko hakan zai kawo ragewar lamarin.