'Yan sanda sun kama mutum 5 da ke kaiwa 'yan bindiga babura, sun ki karbar cin hancin dubu 600 don sakinsu a Kebbi

'Yan sanda sun kama mutum 5 da ke kaiwa 'yan bindiga babura, sun ki karbar cin hancin dubu 600 don sakinsu a Kebbi

Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta samu wata gagarumar nasara ta dakile yawaitar manyan  Laifuka a jihar.

A ranar Jumu'a data gabata hadin gwuiwar 'yan sanda da 'yan banga da ke sintiri a garin Kamba sun yi nasarar kama Saifullahi Suleiman mai shekaru 37 da Halidu Adamu mai shekara 26 da Ibrahim Abubakar dan shekara 37 da Sani Kabiru mai shekara 22 dukkansu a karamar hukumar Dandi a jihar Kebbi a wani baynin sirri da suka samu.

'Yan sandan sun samu babura uku na Honda da ake kira Boko Haram da suka saye miliyan 5,400 a kasar Benin, a binciken da aka yi sun gano an sayi baburar ne domin akaiwa 'yan bindigar Lukurawa ta hannun wani Alhaji dake garin Kangiwa, wanda ake nema a yanzu ya gudu.

Ana cikin bincike wani mutum mai suna Mubarak Ladan dan shekara 28 a garin Kamba ya zo wurin DPO na Kamba SP Bello Mohd Lawal da kuɗi kasa naira dubu dari shidda(600,000) cin hanci yana son a saki wadanda aka kama, anan ne aka yi masa kofar rago bayan karbar kudin da aka rike matsayin shaida, sai aka rike shi.

Kwamishinan 'yan sandan Kebbi CP Bello M Sani ya umarci kataimakin Kwamishinan 'yan sanda gefen binciken manyan laifuka da ya karo kokari a kamo sauran wadanda ake tuhuma a lamarin.

Kwamishina Bello Sani ya jinjinawa DPO na Kamba da 'yan bangar,  kan nuna kwarewa da jajircewa wurin kama mutanen da daura su saman hanyar da jiha ta aminta da ita.

CP ya yi kira ga sauran DPO a Kebbi su yi koyi dana Kamba, su tsaya kan aiki da hada kai don ganin a kawar da bata gari a Kebbi.

Haka ma CP ya roki mutanen gari su cigaba da hada kai da jami'an 'yan sanda da jami'an tsaro don tabbatar da zaman lafiya a jiha.