'Yan Sanda Sun Kama Mutane 79 da Suka Tayar  Da Yamutsi a Zaben Gwamnan Sakkwato

'Yan Sanda Sun Kama Mutane 79 da Suka Tayar  Da Yamutsi a Zaben Gwamnan Sakkwato

 

Rundunar 'yan sandan Sakkwato ta ce jami'an tsaro sun damƙe mutane 79 da ake zargi da karya doka da oda lokacin zaben gwamna da 'yan majalisun jiha. 

The Nation tattaro cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar, DSP Sanusi Abubakar, ya fitar ranar Lahadi. 
Yace wandanda aka cafke sun kunshi mutanen da suka saɓa wa umarnin takaita zirga-zirgan ababen hawa da wasu laifuka da suka saɓa wa dokokin zaɓe. 
A cewarsa, ranar zaɓe hukumomin tsaro sun gamu da Kes kala daban-daban kuma sun kame masu hannu a sayen kuri'u, fasa akwatin zabe, ta da zaune tsaye da barazanar ga zaman lafiyar al'umma da sauransu.
"Duk waɗanda suka aikata laifin da ya saba wa dokokin zaɓe mun gama bincike a kansu kuma mun miƙa su hannun hukumar zaɓe INEC domin ta hukunta su." 
"Ragowar waɗanda suka yi wa dokokin Fenal Kod karan tsaye kuma 'yan sanda sun gurfanar da su a gaban Kotu. 
Har yanzun akwai sauran waɗanda suke karkashin bincike." Kakakin 'yan sandan ya ce kwamishinan hukumar yan sanda ta jihar, Muhammed Gumel, ya roki ɗaukacin mutane da su guji shiga aikata duk abinda ya saɓa wa doka.