'Yan Nijeriya su karɓa da haƙuri, amma ƙarin kuɗin wutar lantarki  na nan tafe - Fadar Shugaban kasa

'Yan Nijeriya su karɓa da haƙuri, amma ƙarin kuɗin wutar lantarki  na nan tafe - Fadar Shugaban kasa

Olu Verheijen, mai ba da shawara ta musamman ga Shugaba Bola Tinubu kan makamashi, ta ce farashin wutar lantarki a Najeriya zai karu cikin ƴan watanni masu zuwa.

A cewar rahoton Bloomberg na ranar Juma’a, Verheijen ta yi wannan bayani ne a taron kolin shugabannin Afirka kan makamashi da aka gudanar a Dar es Salaam, Tanzaniya.

A ranar 3 ga Afrilu, 2024, gwamnatin tarayya ta amince da karin farashin wutar lantarki sau uku ga waɗanda ke karkashin rukunin Band A.

Verheijen ta bayyana cewa dole ne a kara farashin wutar lantarki da kusan kashi 66 cikin 100 domin ya yi daidai da kudin samar da wutar.

Har ila yau, ta jaddada cewa dole ne a daidaita karin kudin wuta da tallafi ga masu karamin karfi, domin hakan zai taimaka wajen kula da tsarin samar da wuta, inganta amincinsa, da kuma jawo hankalin masu zuba jari masu zaman kansu.