'Yan Nijeriya Miliyan 60 Ke Fama Da Tabin Hankali

'Yan Nijeriya Miliyan 60 Ke Fama Da Tabin Hankali

Farfesa Taiwo Obindo, shugaban kungiyar likitocin masu tabin hankali a Najeriya (APN), ya ce sama da ‘yan Najeriya miliyan 60 ne ke fama da tabin hankali.

Obindo, wanda kuma shi ne Shugaban tsangayar ilimin tabin hankali na Kwalejin Likitocin Afirka ta Yamma, reshen Najeriya, ya bayyana haka a wata hira da manema labarai a ranar Lahadi a Abuja.

“Kiwon lafiyar kwakwalwa yana cikin wani hali na nadama ganin cewa muna da ‘yan Najeriya sama da miliyan 60 da ke fama da tabin hankali daban-daban da kuma yadda kusan kashi 10 cikin 100 ne kawai ke samun kulawar da ta dace.

“An bar mu da fiye da kashi 90 cikin 100 da ba za su iya samun kulawa ba kuma ana kiran wannan rukuni tazarar jiyya ga tabin hankali,” in ji Obindo.

Ya ce tazarar ta samo asali ne sakamakon abubuwa daban-daban kamar tazarar ilimin da mutane ba su da bayanan da suka dace game da musabbabin kamuwa da tabin hankali.

Obindo ya ce wasu abubuwan da ke kawo cikas wajen magance matsalar tabin hankali a Najeriya sun hada da imani maganin gargajiya; rashin isassun wuraren kiwon lafiyar kwakwalwa da adadin kwararrun lafiyar kwakwalwa.

A cewarsa, ‘yan tsirarun cibiyoyin kula da lafiyar kwakwalwa suna cikin manyan biranen.

“Sanin cewa kashi 60 cikin 100 na ‘yan Najeriya suna zaune ne a yankunan karkara, ba sa samun kulawar da ta dace kuma suna yin tafiya mai nisa don samun kayan aiki,” in ji Obindo.

Ya kuma ce adadin masu kula da lafiyar kwakwalwa ya yi kadan yayin da ya fadi kasa da adadin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da shawarar.

A cewarsa, ‘yan kalilan da aka horas da su sun kasance suna sha’awar barin kasar.

“Yanayin da muke gudanar da aiki a ciki, yanayin tsaro da kuma albashin da ake ba mutane a kasarnan yakan sa su fita waje.

“Sa’an nan kuma, ba shakka, shine abin da ya jawo kasashen da suka ci gaba suke farautar kwararrun likitocin da aka horar da su a kasarnan, musamman ma na masu tabin hankali,” in ji shi.

Obindo ya ce kudin daukar ma’aikata a kasashe masu karamin karfi ya yi kadan; don haka “ya kasance mafi sauƙi  ga ƙasashen da suka ci gaba don farautar samfuran da aka riga aka yi maimakon horar da irin waɗannan ƙwararru a cikin gida.”

Ya ce akwai bukatar Najeriya ta aiwatar da manufofinta na kula da lafiyar kwakwalwa kan aikin tabin hankali.