'Yan Majalisar Dokokin Sakkwato Sun Mika Buktarsu Ga APC Da Matsayarsu Kan Kakakin Majalisar Jiha

'Yan Majalisar Dokokin Sakkwato Sun Mika Buktarsu Ga APC Da Matsayarsu Kan Kakakin Majalisar Jiha

 

Kiki-kaka da ake ciki a maganar shugavbancin jam'iyar APC a jihar Sakkwato 'yan majalisar dokokin jiha su 13 daga cikin 15 sun mika takadar bukata ga uwar jam'iyarsu ta kasa cewar a mika takardar lashe zabe ga shugaban jam'iya na jiha Alhaji Isah Sadik Achida domin haka ne adalci da kuma cigaban jam'iyya.

 

Wannan bukatar tana kunshe ne a cikin takardar da jagoran mambobin majalisa na APC Bello Isah Ambarura wadda ya mikawa shugabanin jam'iyya na kasa ya ce shugabancin Isah Sadik Achida ne zai kawowa APC hadin kai da karfi da karsashi.

 
A takardar da sakataren jam'iyya John James ya karba a madadin shugaban riko na kasa sun bayyana goyon bayansu ga jagoran jam'iyya a jihar Sakkwato Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da shugaban jam'iya a jiha Isah Sadik da sauran shugabanni da ke tafiyar da jam'iya tsawon lokaci.
 
 A cewarsu shugaban Majalisar dokoki ta Jihar  Aminu Muhammad Manya Achida ya bayyana wani abu da bana gaskiya ba ya ce dukkansu suna goyon bayansa a samar da rabuwar jam'iya a jiha saboda alakar sa da Gwamnatin PDP ta Aminu Waziri Tambuwal a sakkwato.
 
Sun ce Kakakin majalisa shi kadai ke wannan yunkuri nasa ba tare da amincewar mafi rinjayen 'yan majalisar dokokin APC ba.
 
Ambarura ya yi shaguben cewa matsayin na zama shugaban majalisa ba tare da amincewar jagororin APC ya same shi ba  hakan ya sanya Aminu Manya Achida yke aiki tare da Jam'iyyar PDP a Jihar sakkwato abin da  ya sabawa manufofin Jam'iyyar APC da shugabancin ta, saboda haka  Aminu Achida shi kadai ke kidan sa kuma yake rawarsa ba tare da su ba.