'Yan Kannywood sun koka bisa ƙin saka su a  kwamitin rantsuwa na Tinubu

'Yan Kannywood sun koka bisa ƙin saka su a  kwamitin rantsuwa na Tinubu
 
Masana’antar nishadantarwa a arewacin Najeriya, wacce aka fi sani da Kannywood, ta koka bisa ƙin saka mambobinta daga cikin kwamitin rantsar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
 
Sun bayyana rashin jin dadinsu a cikin wata sanarwa, mai dauke da sa hannun wani jarumi kuma mai shirya finafinai,  Al-Amin Ciroma.
 
Sanarwar ta yi nuni da cewa, ƴan Kannywood sun yi kakkausar suka kan zabar ƴan masana'antar fim ta kudancin Nijeriya, wato  Nollywood a kan ƴan Arewa, musamman fitattun  jaruman Kannywood.
 
A cewarsa, abin mamaki ne a ce fitattun ƴan Kannywood irin su Mansura Isah, Ali Nuhu, Abdul Amart, Jamila Nagudu da sauransu, ba su samu shiga cikin jerin sunayen ba, duk da cewa sun yi iya bakin kokarinsu a yakin neman zaben jam’iyyar APC a Najeriya.
 
Sanarwar ta kara da cewa, “mafi yawan wadanda suka shahara a masana’antar fina-finan Hausa, sun yi yakin neman zaben Tinubu tun kafin babban taro.
 
“Tuni dai mashahuran ƴan Kannywood irin su Mansura Isah sun shahara wajen yiwa ‘Jagaban’ yakin neman zabe tun kafin a bayyana shi a matsayin dan takarar jam’iyyar APC.
 
“ni kuwa ina tambayar kwamitin rikon kwarya na Asiwaju me ya sa aka kafa shi ba tare da wani fitaccen dan Kannywood ko daya a jerin sunayen ba?
 
Sanarwar ta kara da cewa "Yawancin jaruman Nollywood da aka sanya a cikin jerin ba su ma nuna fuskokinsu ba a lokacin yakin neman zabe da zabe."