'Yan daba sun kona  ofishin kamfe na Atiku a Gombe

'Yan daba sun kona  ofishin kamfe na Atiku a Gombe

 

A yau Talata ne 'yan daba sun farfasa ofishin Jam'iyar PDP kuma na yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar na 2023 a Jihar Gombe har da sanya mashi wuta.

 

Jaridar The Nation ta rawaito cewa 'yan daban sun farfasa ofishin, inda su ka sace kayaiyaki, su ka farfasa wasu kuma su ka kunna musu wuta, gami da sace abubuwa masu amfani kamar su na'ura mai sanyaya daki da sauransu.

 
Jagoran kamfe din Atiku na shiyyar Arewa-maso-Gabas, Dr Adamu Bappayo ya nuna ɓacin ransa da kaɗuwa a bisa faruwar lamarin.
 
Bappayo, a yayin ganawa da manema labarai a Gombe, ya ce shi bai ga dalilin harin ba sabo da Atiku mutum ne mai son zaman lafiya.
 
"Wajen karfe 2 na dare a ka kira a ke gaya min cewa an kai hari kan ofishin. Ni abinda ya ke ban mamaki shine, ban san me ya sa a ka kai harin ba sabo da shi dai Atiku mutum ne mai son zaman lafiya.
 
"Su na zaman lafiya da gwamnan jihar nan Muhammadu Inuwa Yahaya da ma sauran jama'a daban-daban a faɗin jihar nan," in ji shi.
 
A cewar sa, tuni su ka kai rahoton faruwar lamarin ga rundunar ƴan sanda da ta ƴan sandan farin kaya, inda ya ƙara da cewa hukumomin tsaron sun nemi a kai cikakken rahoto a kan lamarin.