'Yan Daba Sun Faramki Ayarin Gwamna Aminu Tambuwal a Sokoto

'Yan Daba Sun Faramki Ayarin Gwamna Aminu Tambuwal a Sokoto

 

'Yan daba sun kai wa ayarin motocin gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, hari ranar Lahadin nan, 1 ga watan Janairu, 2023. 

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa lamarin ya faru ne lokacin da gwamna Tambuwal da wasu kusoshin gwamnatinsa ke kan hanyar dawowa daga wurin kamfe. 
An ce 'yan daban sun farmaki ayarin Tambuwal, darakta janar da kwamitin kamfen Atiku, yayin da zai koma gida daga wurin gangamin yakin PDP da ya gudana a kananan hukumomin Silame da Wamakko. 
Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta ta ce maharan sun yi amafani da Duwatsu suka rika jifan motocin Ayarin mai girma gwamna.
Sakamakon jifa da duwatsun ne Gilashin kofar gaba na motar SUV ta mai ba Gwamna shawara ta musamman kan harkokin midiya ya farfashe. 
Ya kara da cewa Duwatsun maharan sun yi raga-raga da gilashin gaba na motar babban Sakatataren gwamna, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto. 
Managarciya ta fahimci cewa manyan kusoshin PDP da ke cikin ayarin gwamnan ba su samu ko kwarzane ba sanadiyyar harin. 
Baya ga gwamna Aminu Tambuwal, sauran wadan da ke cikin ayarin sun hada da mataimakin gwamna, Manir Muhamma Dan Iya, dan takarar gwamna a inuwar PDP, Saidu Umar, Abokin takararsa, Sagir Bafarawa da wssu jiga-jigai.