Home Labarai ‘Yan bindigar Lakurawa sun kashe ‘yan canji biyu da sace maƙudan kuɗi...

‘Yan bindigar Lakurawa sun kashe ‘yan canji biyu da sace maƙudan kuɗi a Sokoto

9
0

‘Yan bindigar Lakurawa a ranar Juma’a data gabata sun kawo hari a kasuwar Darusa a yankin Kurdula cikin karamar hukumar Gudu a Sakkwato in da suka kashe masu sana’ar canji guda biyu suka sace maƙudan kuɗi da ba a san yawansu ba.
Wani mazauni yankin ya shaidawa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun shigo kasuwar ne saman babura hudu kowane da goyon mutum ɗaya su Takwas kenan, dauke da bindigogi in da suka tafi wurin masu sana’ar canji “anan take suka kashe Alhaji Ummaru Darusa da Muhammad Sani, bayan nan suka kwashe kuɗaɗen da suke mu’amala da su, suka tafi abinsu.”
Ya ci gaba da cewa “kasuwar tana tsakanin Nijeriya da Nijar ne mutanen ƙasashen biyu suna harkokin kasuwanci anan, shi ɗan canji Sani Hakimi ne a Nijar amma a kasuwar yake kasuwancinsa na canji da wasu harkoki.
“Mun zargi ‘yan bindigar sun daɗe suna bibiyar Ummaru sai yanzu ne suka samu damar shi suka kashe tare da abokin sana’arsa, sun tafi da kuɗinsu da suke sana’a wanda akwai kuɗin Nijeriya da ƙasashen waje kuɗi ne masu yawa sosai.
Ya yi kira ga jami’an tsaro su riƙa yin sintiri a wurin domin suna fama da ƙarancin jami’an a yankin.
‘Yan bindigar Lakurawa sun daɗe suna cin karensu ba babbaka a yankin in da suke zartar da hukuncin da suke so a ƙauyukkan dake yankin Gudu da Tangaza.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Sakkwato Ahmad Rufa’i ya tabbatar da faruwar lamarin “amma ranar Alhamis ne abin ya faru ‘yan bindiga sun kawo hari a garin Darusa suka kashe mutum biyu, Alhaji anan take ya rasu amma ɗayan sai da aka kai shi asibitin Dogon dutse sannan ya bar Duniya,” a cewarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here