'Yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aurata da ƴarsu a Katsina
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari da safiyar Talata a unguwar Filin Canada Quarters da ke Sabuwar Unguwa a Katsina, inda suka yi garkuwa da wani matashi, Anas Ahmadu, matarsa mai juna biyu Halimat, da kuma ‘yarsu.
Daily Trust ta rawaito cewa a yayin harin, wani ɗan sa-kai mai suna Abdullahi Muhammad, mai shekara 25, ya rasa ransa bayan ya je domin taimakawa.
Rahotanni sun ce maharan kusan bakwai ne suka kewaye gidan da ƙarfe 3:00 na dare, suka balle ƙofa sannan suka yi awon gaba da iyalin.
An gano cewa matar da aka sace ‘ya ce ga shahararren dillalin man fetur a Katsina, Alhaji Usman Turare.
Majiyoyi sun ce maharan sun tuntubi kawun matar da yammacin ranar, amma ba a tabbatar ko sun nemi kudin fansa ba.
Kakakin ‘yansanda a jihar, DSP Abubakar Sadiq, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro sun hanzarta zuwa wurin tare da ɗaukar matakan bincike domin ceto waɗanda aka sace da kuma kamo maharan.
Harin ya jefa mazauna Katsina cikin fargaba, yayin da ake ƙara kiran gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara tsaurara matakai kan yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
managarciya