Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban ilimin likitanci sama da 20 a Benue
'
Sama da daliban koyon ilimin likitanci da likitancin hakora su 20 tare da wani jami’i wasu ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su a jihar Benue.
Daliban su na kan hanyar su ne ta zuwa taro a Enugu, yayin da aka yi musu kwanton bauna da misalin karfe 5:30 na yamma a garin Otukpo, inji rahoton Vanguard.
Rahotanni sun bayyana cewa wadanda harin ya rutsa da su sun fito ne daga Jami’ar Maiduguri da kuma Jami’ar Jos.
Kakakin Rundunar Ƴansandan Jihar Benue, SP Catherine Anene, ta tabbatar da sace mutanen tare da bayyana cewa suna kan bincike.