Da yammacin jiya Juma’a 6 ga watan Fabrairun 2026 wasu ’yan bindiga suka kai mummunan hari a kauyen Kiratawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
Lamarin ya tayar da hankulan al’ummar yankin wanda aka ce harin ya yi sanadin rasa wani liman da kuma dagaci lamarin da ya tarwatsa jama’ar yankin baki daya.
Rahoton Bakatsine da ke kawo bayanai kan lamuran tsaro a Arewacin Najeriya shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Asabar 7 ga watan Fabrairun 2026.
Ana yawan samun hare-haren ta’addanci a yankunan Sokoto da ake alakantawa da yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji da ya zama annoba a Arewacin Najeriya.
Bayan kisan limamin, maharan sun nufi hanyar Takatsaba inda suka yi kwanton-bauna a gadar Dangulbi, suka harbe wani mutum guda wanda ya rasa ransa nan take.
Rahotanni sun nuna cewa harin bai dauki lokaci mai tsawo ba kafin jami’an tsaro su isa yankin, lamarin da ya tilasta ’yan bindigar tserewa daga yankin domin tsira da rayukansu.
Majiyoyi sun bayyana cewa tun bayan kisan Kallamu, wani babban mataimaki ga shahararren dan bindiga Bello Turji, ba a sake samun wani hari a wannan hanya ba sai jiya.
Harin ya tayar da hankalin al’ummar yankin, inda ake kira ga hukumomi da su kara tsaurara matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a wadanda suke shan fama kan hare-haren.
Wasu majiyoyi suka ce ’yan bindiga da ake zargin suna biyayya ga shahararren jagoran ta’addanci Bello Turji sun kashe dagacin kauyen Magarau.





