'Yan bindiga sun tarwatsa gari 17 a Kebbe, mutane na naman agajin gwamnatin Sokoto

'Yan bindiga sun tarwatsa gari 17 a Kebbe, mutane na naman agajin gwamnatin Sokoto
 
 
Masu kishin ƙaramar hukumar Kebbe a jihar Sakkwato sun yi kira ga gwamnati ta sakarwa karamar hukumar su kudadenta na wata wata da gwamnatin tarayya ke bayarwa domin magance matsalar tsaro da ta addabi yankin wanda ya yi sanadin korar mutane a kauyukka 17.
 
Mutanen  suna son gwamnatin Sakkwato ta bari karamar hukuma ta amfana da kudadenta hakan zai taimaka ga magance matsalar  tsaro tun a matakin kasa.
 
Mai magana da yawun masu kishin Alhaji Haruna Adamu Kebbe ya soki Gwamnatin jiha da karamar hukuma kan fita batun mutanen da matsalar tsaro ta addaba, matakin da gwamnati ke dauka ba ya isa akwai jan kafa a harkar tsaro da bayar da tallafin rage radadi a yankin Kebbe.
 
Haruna ya nuna gamsuwarsa matukar karamar hukuma za ta yi amfani da kudadenta yanda yakamata tana iya samar da abubuwan walwala ga mutanen da harin 'yan ta'adda ya rutsa da su da kuma rage matsalar tsaron da ta ta'azara. 
 
Mutanen sun zargi 'yan bindigar Lakurawa ne suka mamaye masu karamaramar hukuma abin da yakai da tayar da gari 17 a yankin na Kebbe aka kashe mutane da dama da sace dabbobi da yin garkuwa da mutane, abin da ya sanya daruruwan mutane yin gudun hijira a makwabtan jihohi.
 
"Yanzu haka suna rike da wani dan kasuwa sun ce sai an bayar da miliyan 10 za su sake shi, yana wurinsu har ya samu matsalar shanyewar rabin jiki amma sun ki sakinsa dole sai an kawo kudin, sun hana girbe amfanin gona a yankin Fakku 'yan bindigar suna yin yanda suka ga dama, har yanzu ba mu iya kididdige yawan mutanen da ke hanunsu."
 
Kan haka mutanen suke kira ga gwamnatin tarayya ta ba su damar mallakar makamai domin kare kansu ga wadannan batagarin.
 
A taron manema labarai da mutanen suka kira a sakatariyar 'yan jarida dake Sakkwato a ranar Assabar sun fitar da damuwarsu cewa "Ba mu iya bacci idon mu biyu a rufe, an tarwatsa mutanenmu kuma gwamnati ba ta yin abin da yakamata a wurin kare mu".
 
Jihar Sakkwato na fama da mtasalar tsaro ta 'yan bindiga masu satar shanu da Lakurawa da su Bello Turji abin da ya mamaye kananan hukumomi 21 daga cikin 23 na jihar Sakkwato.
 
Masu sharhi na ganin akwai bukatar gwamnati ta sake salon da take amfani da shi a wurin yakar 'yan bindigar domin samun sakamako mai kyau cikin kankanen lokaci.