Home Labarai ‘Yan bindiga sun saki Mata da Ɗan Shugaban APC a Kebbi

‘Yan bindiga sun saki Mata da Ɗan Shugaban APC a Kebbi

11
0

ʼYan bindiga sun sako matar Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙaramar Hukumar Yauri a Jihar Kebbi, Hajiya Aisha Yusuf Alhassan, da ɗansa Sunusi Yusuf Alhasan bayan shafe kwanaki takwas a hannun masu garkuwa da mutane.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wani ɗan jarida a yankin Al-amin Ushe ya ce, an sako su ne a daren Talata, amma har yanzu ba a bayyana yadda aka kuɓutar da su ba.

An yi garkuwa da Hajiya Aisha Yusuf Alhassan da Sunusi Yusuf Alhasan ne a ranar 22 ga Yuni, 2026, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kutsa gidan Yusuf Alhasan da ke unguwar Low Cost a garin Yauri tare da yin awon gaba da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here