‘Yan bindiga sun sace ‘yan gudun hijirar da suka koma gidajensu a jihar Sokoto
Wasu ‘yan gudun hijira da suka koma ƙauyukansu kwanan nan sun faɗa hannun ‘yan bindiga a wani sabon harin da aka kai ƙauyukan Gasalodi da Tungar Barke da ke Ƙaramar Hukumar Tambuwal a Jihar Sokoto ranar Laraba.
Rahotannin da jaridar Daily Trust ta samo sun ce maharan sun yi garkuwa da mutane da dama yayin harin.






