'Yan Bindiga Sun Sace  Na Hannun Daman Gwamna Matawalle a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Sace  Na Hannun Daman Gwamna Matawalle a Zamfara

 

Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan fashin daji ne sun yi garkuwa da mai baiwa gwamna Bello Matawalle shawara ta musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Ma’aji. 

Tribune ta ce yan bindigan dajin adadi mai yawa sun kutsa gidan hadimin gwamnan da farkon awanni ranar Asabar a Anguwar Mareri, cikin kwaryar birnin Gusau.
Babban ɗan hadimin gwamnan, Lukman Ibrahim, ya tabbatar da labarin garkuwa da mahaifinsa har gida a Gusau, babban birnin jihar Zamfara. 
A cewar Lukman, mahaifinsa na cikin ɗakinsa lokacin da maharan suka diro cikin gidan ta katanga. 
A kalamansa ya ce: "Ina cikin ɗaki lokacin da na ji wani ya diro cikin gidanmu, nan take na fito na duba waye kawai yan bindiga suka cafke ni." 
"Suka tilasta mun na kaisu ɗakin mahaifina kuma daga nan, suka yi awon gaba da shi zuwa mafakarsu da ba'a sani ba."
 A rahoton Dailypost, Lukman ya kara da cewa tun da wuri-wuri aka kai rahoton abinda ya faru ga hukumar yan sanda domin ɗaukar mataki kan yuwuwar ceto hadimin gwamnan. 
Yayin da aka tuntubi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, ba'a sami lambarsa ba, wayar tarho ɗinsa a kashe har kawo yanzu da muka haɗa wannan rahoton.