‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 50 A Kaduna
Jaridar Punch ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi barna a wani kauye da ake kira Damari a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Wannan rahoto mara dadi ya fito a karshen makon da ya wuce, cewa ‘yan bindigan sun yi sanadiyyar mutane na barin kauyen Damari.
Ana maganar ‘yan bindigan sun yi awon-gaba da mutane kimanin 50 dake zaune a kauyen Damari.
Daily Trust ta kawo wannan labari a wani rahoto. Shugaban kungiyar Birnin-Gwari Emirate Progressives’ Union, Ishaq Kasai, ya tabbatar da wannan a wani jawabi da ya fitar a daren ranar Lahadi.
Ishaq Kasai yake cewa a ‘yan kwanakin bayan nan, ana ta kawo masu munanan hare-hare a sanadiyyar tashin ‘Yan kungiyar Ansaru na Boko Haram. A lokacin da suke nan, Sojojin kungiyar ta’addan na Ansaru sun kasance suna taimakawa wajen hana a kawo hare-hare a kauyukan da ke yankin.
“Abin takaicin da ya faru a awanni 72 da suka wuce a garin Damari, mazabar Kazage da ke gabas da Birnin Gwarin jihar Kaduna ya kai intaha.
Zuwa ranar Asabar, ‘yan bindiga suka zagaye Damari, suka yi awon-gaba da kusan mutane 50.
Kafin nan, sojoji daga Dogon-Dawa sun shiga garin, suka raka mazaunan da suka rage da ke da niyyar tserewa wasu makwabta, wasu har Zaria.” - Ishaq
Kasai Kasai yace mafi ban takaici shi ne wata mai juna biyu da ta tsere tare da mutane da aka bari yayin da ta fadi, ta haifi jariri, amma a karshe duka suka mutu.
Ana haka ne kuma muka samu labari cewa ‘yan bindiga sun shiga garin Shika da ke karkashin karamar hukumar Giwa, suka dauke wasu Bayin Allah.
Kamar yadda majiyarmu ta shaida mana, ‘yan bindigan sun auka wani gida ne a Layin Maje da ke Shika Gari, suka dauke magidanci, matarsa da yaro.
managarciya