'Yan Bindiga Sun Sace Matasa Maza da Mata 80 a Jihar Zamfara 

'Yan Bindiga Sun Sace Matasa Maza da Mata 80 a Jihar Zamfara 

'

Matasan da basu gaza 80 ba da suka shiga cikin Jeji ɗebo Itatuwan girki sun shiga hannun 'yan ta'adda da ake zaton sun yi garkuwa da su a jihar Zamfara. 

Vanguard ta rahoto cewa lamarin, wanda ya auku a ƙauyen Wanzamai da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar Jumu'an nan ya jefa mutanen ƙauyen cikin firgici da tashin hankali.
Duk wani yunkurin jin ta bakin rundunar 'yan sandan jihar ko gwamnatin Zamfara ya ci tura har zuwa yanzu da muke haɗa muku wannan rahoton.
Amma iyayen da aka yi garkuwa da 'ya'yansu sun shaida wa BBC Hausa a wata hira cewa yan ta'addan sun sace matasan yaransu maza da mata yayin da suka je ɗebo Itace a Jeji.
A cewar wani mahaifi, 
"Lamarin ya shafi kowa a kauyen, ko dai ɗanka ko ɗiyarka na cikin wadanda ke tsare a hannun yan ta'adda, ko kuma ya'yan yan uwanka. Ni kaina sun tafi da ɗana da Babur ɗina." 
Wata mata a ƙauyen Wanzamai ta ce ɗiyarta yar shekara 15 a duniya na cikin waɗanda aka yi garkuwa da su. 
"Mun shiga damuwa saboda bamu san halin da 'ya'yanmu ke ciki ba a hannun yan bindiga," inji ta. 
Har kawo yanzun da muka kawo muku wannan labarin 'yan ta'addan ba su tuntubi kowa game neman kuɗin fansa ba.
Bayanai sun nuna cewa 'yan ta'adda sun kai hari a baya farkon watan Ramadan kan mazauna kauyen Wanzamai amma dabbobi kaɗai suka sata suka yi gaba.