Wasu ƴan bindiga sun shiga garin Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Katsina, sun yi garkuwa da mahifiyar Dauda Kahutu Rarara.
Rahotannin da Managarciya ta samu da safiyar ranar Jumu’a sun nuna cewa maharan sun ɗauki mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar, a jiya Alhamis da daddare.
Mazaunan Kahutu sun bayyana cewa ƴan bindigar na ɗauke da manyan bindigu lokacin da suka shiga garin don haka ba a iya tunkararsu ba.
Ganau sun ce maharan sun kutsa sabon gidan da Rarara ke ginawa a garin Kahutu da karfe 1:00 na dare, suka yi awon gaba da datijuwar, Hajiya Halima Adamu. Ana zargin dai ƴan bindigar ba su zo da abin hawa ba, kuma duk da sintirin da ƴan banga ke yi a garin, maharan sun ɗauki dattijowar ba tare da fuskantar turjiya ba.
Ɗaya daga cikin masu aikin gini a gidan Rarara ya shaidawa wakilin Legit Hausa cews ƴan bindiga sun shiga gida ta wata babbar taga da ba a kammala aiki ba.
