'Yan Bindiga Sun sace mahaifiyar Mawaki Rarara

'Yan Bindiga Sun sace mahaifiyar Mawaki Rarara

Wasu ƴan bindiga sun shiga garin Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Katsina, sun yi garkuwa da mahifiyar Dauda Kahutu Rarara. 
Rahotannin da Managarciya  ta samu da safiyar ranar Jumu'a sun nuna cewa maharan sun ɗauki mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar, a jiya  Alhamis da daddare. 
Mazaunan Kahutu sun bayyana cewa ƴan bindigar na ɗauke da manyan bindigu lokacin da suka shiga garin don haka ba a iya tunkararsu ba. 
Ganau sun ce maharan sun kutsa sabon gidan da Rarara ke ginawa a garin Kahutu da karfe 1:00 na dare, suka yi awon gaba da datijuwar, Hajiya Halima Adamu. Ana zargin dai ƴan bindigar ba su zo da abin hawa ba, kuma duk da sintirin da ƴan banga ke yi a garin, maharan sun ɗauki dattijowar ba tare da fuskantar turjiya ba. 
Ɗaya daga cikin masu aikin gini a gidan Rarara ya shaidawa wakilin Legit Hausa cews ƴan bindiga sun shiga gida ta wata babbar taga da ba a kammala aiki ba.