'Yan Bindiga Sun Sace Mace Tana Kan Gadon  Jinya A Kaduna

'Yan Bindiga Sun Sace Mace Tana Kan Gadon  Jinya A Kaduna

 

Masu garkuwa da mutane sun sace wata matar aure dake jinya a dakin mijinta a anguwar Malamai, kauyan Kakeyi dake gundumar Demba a karamar hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.

 
Anguwar Malamai ita ce anguwar da Babban Dam din Zariya yake kuma Yana da tazarar kimanin kilomita daya tsakanin shi da gidan talabijin na kasa, NTA Zariya.
 
Wani Mazaunin Kauyen da Bai so a bayyana sunan sa saboda halin tsaro, ya sanarda wakilin Aminiya cewa Maharan wadda suka dira anguwar da misalin karfe goma sha biyu na daren laraba cikin mota,sun wuce ne Kai tsaye zuwa kofar gidan wani mai suna Alhaji Shaibu Dallatu.
 
A cewar sa bayan sun Isa gidan sun sami yara masu kwana a shagon gidan idan suka tambaye su ko mai gidan yana nan sa'ilin da yaran suka amsa musu cewar yana nan.
 
Majiyar taci gaba da bayanin cewa ashe lokacin da su maharan suke tambayar yaran, shi mai gidan yaji su tunda dama yana cikiba dakin mai dakin sa Yana jinyar ta, daga nan baiyi wata wata sai ya haura Katanga ya fita ta baya.