‘Yan Bindiga Sun Kori Mutanen ƙauyuka 5 da Sace Shanu Sama da 100  a  Sokoto

‘Yan Bindiga Sun Kori Mutanen ƙauyuka 5 da Sace Shanu Sama da 100  a  Sokoto

 

Mazauna wasu Kauyukkan  da ake kira  Ungusi, Asarara, Sangi, Mai Kurfana, da Gwandi duk cikin karamar hukumar Kebbe a Sokoto  'yan bindiga suka fatattake su dubban mutane  sun rasa matsugunansu inda wasu da ba a tantance adadinsu ba aka ruwaito wasu mahara da ake kyautata zaton barayi ne suka sace dimbim shanu sama da 100 kashe.

 
wata majiyar ta ce ‘yan bindigar sun kori  al’ummomi da yawa  a  karamar hukumar.
 
Ya ce yana kyautata zaton ‘yan bindigar sun fito ne daga jihohin Zamfara, Kebbi, da Neja da ke makwabtaka a Sakkwato in da ake ci gaba da gudanar da ayyukan soji, kuma a yanzu ‘yan bindigar sun samu mafaka Kebbe a saboda  ciyayi dake yankin.
 
 Ya ce wannan lamarin  zama ruwan dare a kowace shekara a karamar hukumar  ‘yan bindigar  suna zuwa suna addabar kauyuka, suna sace musu dabbobi, da amfanin gona tare da raba da dama daga muhallansu.
 
Ya kuma roki gwamnatin tarayya da ta sa baki ta hanyar aikin soja kamar yadda aka yi shekaru uku da suka wuce.
Wata majiyar ta ce a ko a yau(Talata) da nake magana da ke 'yan bindigar sun koma Gwandi in da suka hana mutane cire amfanin gonarsu, bayan sace masu shanu da suka yi.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Sanusi Abubakar, ba a samu magana da shi ba kan lamarin.